Wani sabon bincike da aka gudanar a kasar Amurka ya bayyana yadda wani sinadari da masana binciken kimiyya su kai wa lakabi da THC, wanda ake samu cikin ganyen wiwi yake bayyana a nonon mace mai shayarwa koda kuwa ta kwashe kwanaki shidda bata sha tabar wiwi ba.
Binciken ya nuna yadda ake samun sinadarin THC, a nonon mace mai shayarwa kuma masana sun bayyana cewa kasancewar wannan sinadari a kwakwalwar jinjiri na shafar habakar ta, lamarin da ka iya haifar da mummunar illa ga yara.
Ku Duba Wannan Ma Indra Nooyi Shugabar Kamfanin PepsiCo Zata Yi MurabusA cewar Christian Chambers, babbar farfesa kuma likiciya data kware a fannin kananan yara a jami'ar San Diego dake jihar California, kuma wadda ta jagoranci wannan bincike, ta bayyana cewa ba a san takamaiman yawan adadin wannan sinadari da ka iya haifar da illa a kwakwalwar kananan yara ba.
Daga karshe ta bayyana cewa bai dace a ce ba cikakkiyar masaniya akan wannan matsala ba, amma a cewarta, shawara ga mata masu ciki da masu shayarwa kawai ya daganta da irin tabbacin da aka samu idan an yi masu gwaji, ta kuma kara da cewa wannan matashiya ce kawai domin a gaggauta daukar mataki domin gudanar da muhimmin bincike domin shawo kan wannan lamari kafin ya zama da muni.