Rohotanni sun bayyana cewa hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya zata kara inganta tsaro a cikin sakateriyar hukuma kula da kwallon kafa ta Najeriya, domin kiyaye rikici da kuma tare yan’adawa daga shiga Sakateriyar.
A lokacin da rikici ya barke tsakinin Chris Giwa da Amaju Pinninck akan wanda zai shugabanci hukumar kwallon kafa ta Najeriya. A zaben da akayi a Abuja a ranar 26 ga watan Augustan 2014, an bayyana Giwa a matsayin wanda ya lashe zaben kuma shine zai shugabanci kungiyar. Daga bisani shima Pinnick ya ci gaba da shugabanncin kungiyar a zaben 30 ga Satunba 2014 wanda akayi a Warri.
Mutanen Giwa sun mamaye Sakateriyar a ranar 2 ga watan yuli bayan da Ministan matasa da wassannin Solomon Dalung, ya umarci Gwamnatin Tarayya da ta amince da hukuncin da babbar kotun Najeriya ta zartar a ranar 27 ga watan Afirilu domin watsi da zaben da yaba Pinnick shugabancin kungiyar.
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta dauki wannan matakinne bisa ga dokar da gwamati ta bada bayan da shugaban FIFA Gianni Infantino ya fada a ranar 13 ga watan yuli cewa su dai Amaju Pinnick ne kadai suka sani a matsayin shugaban hukumar kallon kafa ta Najierya.
Facebook Forum