Indra Nooyi, ‘yar shekaru 62 da haihuwa ta sanar da cewa zata yi murabus a watan Oktoba daga matsayin shugabar babban kamfanin PepsiCo bayan ta yi shekaru 12 tana shugabancin kamfanin. Za ta cigaba da kasancewa shugabar kamfanin har zuwa farkon shekara mai zuwa.
Wannan sanarwar ta kawo karshen aikin da Indra, 'yar kasar India ta yi a kamfanin PepsiCo na tsawon kusan shekaru 25, wadda ta kasance shugaba mai kwazo a cikin wadanda suka jagoranci manyan kamfanoni 500 a duniya da ake kira Fortune 500 da turanci.
Kudaden shiga na kamfanin sun kusan linkawa a karkashin shugabancin ta a lokacin da ta kai kamfanin zuwa matakin da wasu kamfanoni suka sanya hanun jari.
Indra Nooyi, ta fadawa kamfanin yada labaran Bloomgerg cewa tana shirin karfafawa kamfanoni gwiwa su ba mata damar aiki a manyan mukamai. Yanzu haka, mata ke shugabanci a kamfanoni 24 a cikin 500 da aka sanya sunayensu a jaridar Wall Street.
A cewar tashar harkokin kasuwanci ta CNBC, 4 daga cikin manyan kamfanonin harkokin tsaro na Amurka guda 5, mata ne zasu jagorance su kwanan nan: wato Northrop Grumman, da Lockheed Martin, da General Dynamics, da Boeing Defense, da kuma Space and Security.
Facebook Forum