A jiya ne Talata musulmai a duk fadin duniya suka gudanar da bukukuwan Sallah Babba, biyo bayan kammala aikin hajji da akayi, wanda hakan yake cikin rukunnan musulunci. Bukin sallah babba na daya daga cikin muhiman bukukuwa a addinin Islama.
Hakama a kasar Amurka musulmai daga kowane bangare na kasar sun gudanar da bukukuwan nasu kamar kowa, amma a karamar hukumar Burke a cikin jihar Virginia ta Amurka, al’ummar wannan karamar hukumar sun gabatar da sallar idin su a wata katafariyar Coci.
Limamin wannan masallacin Malan Yousef Zerwal, dan asalin kasar Moroco, ya jagoranci sallar kuma ya gabatar da huduba a karshe, inda yake nuna cewar lallai da ace mutane a duniya zasu zama masu mutunta addinan kowa batare da nuna wata kiyayya a junaba, lallai da yanzu duniya ta zama wajen zama ga kowa, kuma da yanzu babu duk matsalolin da ake fama dasu a fadin duniya.
Sai ya kara da cewa yanzu munyi sallah a cikin coci, Allah baya lura da inda mukayi sallar mu, yana amfani ne da abun dake cikin zukatan mu, ashe kuwa ya kamata mutane mu rika girmama kowa muna ba kowa girman da Allah ya bashi, maganar cin zarafi ko kiyayya ba abuce da ya kamata ace an samu a cikin al’umma ba musamman ta musulmai.
Domin kuwa Addinin islama yana koyar damu girmama juna da darajarta kowa, kana da ba kowa hakkin sa, don haka ya kamata mutane a fadin duniya su dauki sauran abokan tarayyar su da suke wasu addinai su karrama su, domin kuwa duk abubuwa da suka kamata Muslumi ya nuna a duk inda ya sami kanshi, shine ya tabbatar da cewar Allah na kallon shi, kuma ya sani duk wani abu da zaiyi wanda zai batama addinin suna to ya guje shi.
Shugaban cocin kuwa Mr. Heflin, cewa yayi dukkan mu mabiya addinan Islama, yahudu da nasara, Cirista dukkan mu munyadda da Allah daya, don haka ba wani abu mai wuya bane a gare mu baki daya, idan munyi maraba da wasu manbiya addinan a wajajen ibadun.
Limamin yayi kira da musulmai a duk inda suke a fadin duniya su dinga tunawa da kuma yin addu’a ga duk sauran Musulmai da suke a fadin duniya suna fuskantar wasu wahalhalu, kamar kasashen Yemen, Syria, Iraq da ma Najeriya.
Facebook Forum