Jami'an gwamnatin jahar Kaduna da na tarayya da dama ciki har da hafsan hafsoshin Sojan kasan Najeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, na ci gaba da shiga garin Tudun Biri inda wannan Ibtila'in ya faru don jajantawa, yayin da 'yan-uwa da iyalan wadanda su ka rasa rayukansu ke shaidawa duniya cewa wasu daga cikin wadanda suka ji rauni da ke jinya a asibiti ma sun kara rasuwa.
Rahinatu Zubairu ta ce 'yan-uwan ta 14 ne su ka rasu a wannan hari, kuma wasu na asibiti. Ita ma dattijuwa Aisha Jibrin ta ce yanzu haka ita kadai ce ta rage saboda duk an kashe mata 'ya'ya.
Tawagar gwamnatin jihar Kaduna ta shiga garin Tudun Biri tun a ranar Talata, kuma mataimakiyar gwamnan Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta ce duk da yake gwamnatin Kaduna kadai ba za ta iya biyan diyyar dukkan mutanen da su ka rasu ba, amma za ta jajirce don ganin an taimaki al'ummar da wannan ibtila'i ya shafa.
Sai dai kungiyar Jama'atu Nasrul-Islam (JNI) ta kasa, ta ce wajibi ne gwamnati ta biya diyyar rayukan da aka rasa baki daya, inji sakataren kungiyar farfesa Khalid Abubakar Aliyu.
Ita kuwa kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) reshen jahar Kaduna, cewa ta yi akwai bukatar daukar mataki kan wannan hari don kiyaye gaba, kamar yadda shugaban kungiyar, Rebaren Joseph John Hayab ya shedawa Muryar Amurka.
Tuni dai gwamnatin tarayya ta ba da umarnin bincike kan wannan hari da sojan kasan Najeriya su ka ce kuskure ne aka samu, lokacin aikin fatattakar 'yan-bindigan da su ka addabi wannan yanki.
Domin Karin bayani saurari rahotan Isah Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5