Rundunar sojan Najeriya a Kaduna ta hanyar gwamnatin jihar ta dauki alhakin kai harin amma ta ce cikin kuskure ne.
Tun farko rundunar sojan saman Najeriya ta nesanta kan ta daga harin da cewa, ba ita kadai ke amfani da jirage marar matuka a rundunonin tsaro a arewa maso yamma ba.
Faruwar wannan akasi ya jawo juyayi da kuma neman binciken yanda a ka samu kuskuren don kaucewa hakan a gaba.
Kungiyar ANSARUL-DIN-ATTIJJANIYYA da ke kula da 'yan darikar Tijjaniyya a Najeriya kuma ke gudanar da maulidi, ta bukaci daukar matakan zahiri kan akasin da ya auku.
A hirar shi da Muryar Amurka, babban sakataren kungiyar Mallam Alkassim Yahaya Yawuri ya ce su na bukatar diyyar mutanen da a ka rasa da kula da jinyar wadanda su ka samu raunuka.
Ba wannan ne karon farko da aka sami rin wannan kuskure ba, don ko a shekarun baya, wani jirgin sojan saman Najeriya ya sauke bom kan sansanin 'yan gudun hijira a Rann da ke Borno inda kimanin mutum 50 su ka rasa ran su.
Saurari rahoton :
Dandalin Mu Tattauna