Kasashen dai sun rattaba hannu ne a kań yarjejeniyar shiga cikin aikin na bututun iskar gas don samar wa kasashen nahiyar Afrika sauki a matsalolin makamashi, lantarki tare da bunkasa tattalin arzikin nahiyar.
A yau juma’ah 16 ga watan Yunin shekarar 2023 da muke ciki ne karin kasashe 11 suka shiga sahu a wajen sanya hannu a kan yarjejeniyar aikin bututun iskar gas da kamfanin NNPCL na Najeriya da gwamnatin kasar Morocco suka fara rattaba hannu a kai a cikin watan Satumban shekarar 2022 karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Da farko an yi yarjejeniyar ce tsakanin kasashe biyu wato Najeriya da Morocco sai kuma kungiyar ECOWAS mai kula da tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma a cikin babban birnin kasar Morocco a wancan lokacin.
Ko mece ce ma’anar samun karin kasashen nahiyar Afrika 11 da suka shiga wannan yarjejeniya ke nufi ga asalin aikin bututun iskar gas din, shugaban kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya, Mal. Mele Kyari ya ce aiwatarwa na nufin cewa kasashen Afrika sun hada kansu wuri daya don a tabbatar da bututun iskar gas din ya tashi daga Najeriya ya shiga kasashe 11 kafin ya shiga kasar Morocco tare da wasu kasashe 4 da basa cikin tsarin yarjejeniyar tun farko.
Babbar darakta a ofishin ma'adinai na kasar Morocco, Amina Benkhadra, ta ce sarki Muhammad na 6 na kasarta tare da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne suka kaddamar da wannan gagarumin aikin bututun iskar gas din da zai rika fitowa daga Najeriya zuwa kasar Morocco sannan a fitar zuwa kasashen Turai, tana mai cewa wannan muhimmin aikin zai taimaka wajen kawowa da kuma hanzarta samar da wutar lantarki ga mutanen nahiyar Afrika miliyan 100; zai kuma kara habaka masana'antu a wannan nahiya mai kasashe masu dimbin albarkatun kasa da aikin noma baya ga samun isasshen makamashi na yau da kullum mai dorewa.
Kazalika, Amina Benkhadra ta ce wannan muhimmin aikin zai ba da gudummawa ga haɗin kai a yankin Nahiyar Afrika musamman ma cimma buƙatar haɗa kan ƙasashe a Afirka ta Kudu baya ga kawo ci gaba a fannin zamantakewa, samun karin masana'antu da bunkasa tattalin arziki sai kuma bai wa nahiyar matsayi mai girma a cikin sauran kasashen duniya.
Shi ma kwamishina a fannin abubuwan more rayuwa, makamashi da tsarin fasahohin zamani a kungiyar ECOWAS, Mal. Sediko Douka, ya ce idan aka aiwatar da aikin bututun iskar gas din yadda ya kamata za a rage matsalolin da suka shafi wutar lantarki kumą kungiyar ECOWAS dole ta kasance kan gaba a wannan aikin ba tare da yin kasa a gwiwa ba.
A aikin Za a dauko bututun iskar gas din ne daga tsibirin yankin Brass na Najeriya kuma ya kai ga arewacin kasar Maroko, inda za a haɗa shi da bututun Maghreb na Turai wato MEP wanda ya samo asali daga kasar Aljeriya da Morocco har ya zuwa kasar Sifaniya.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5