Kwamandan sojoji na musamman dake garin Doma a jihar Nasarawa, Manjo Janaral M.G.Ali ya shaidawa muryar Amurka cewa tun watanni takwas da suka gabata kungiyar ta rikide zuwa ta Boko Haram.
Janaral Ali ya ce suna da bayanan sirri cewa a baya jagoran Boko Haram Abubakar shekau ya tura wakilinsa zuwa Darussalam inda ya nemi su karbi akidar Boko Haram.
Da suka ki yarda, mayakan shekau suka yiwa jagororin na Darussalam kisan gilla inda suka amshe jagorancin sansanin kafin daga bisani sojoji na musamman suka tarwatsasu.
Amma Ohinoyi na Dausu, Alhaji Idriss Hakimin Dausu dake Kasar Toto ya shaidawa Muryar Amuka cewa har yanzu akwai sauran ‘yan wannan kungiya a yankunansu, domin a halin yanzu basu isa suje gonakinsu ba, don gudun kama su a yi garkuwa dasu sai an biya makudan kudi.
Kwamishinan watsa labarai na jihar Nasarawa Mr. Dogo Shamman ya ce za a maida iyalan wadanda aka tarwatsa ga gwamnatocin jihohinsu daban daban, su kuma ‘yan asalin jihar za a tattara su wuri guda kafin a san yadda za ayi dasu.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina cikin sauti
Your browser doesn’t support HTML5