Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Karar Shugaba Buhari Kan Naira Biliyan 800


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Kungiyar kwato wa talaka hakkokin su da tabbatar da adalci (SERAP) ta maka Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja.

SERAP ta maka shugaban kasar ne saboda ya gaza bayyana sunayen mutanen da gwamnati tace ta kwato Naira Biliyan 800 (N800bn) daga wajensu, da kuma ayyukan da aka yi da kudaden.

Sanarwar shigar da karar Shugaba Buhari a Kotun na dauke da sa hannun Mukadashin Shugaban Kungiyar SERAP Kolawole Oluwadare wanda ya ce suna neman kotu ta umurci Shugaba Buhari ya wallafa sunayen mutanen da aka kwato kudaden daga wajensu, sanan kuma a wallafa ranaku da wuraren da aka yi ayyuka da kuma irin ayyukan da aka yi.

Kungiyar ta kuma bukaci bayani daga Ministan shari'a na kasa Abubakar Malami, da kuma Ministar kudi Zainab Ahmed.

Ministar Kudi Zainab Ahmed

Kungiyar SERAP dai ta yi amfani da 'yancin neman bayanai da dokar kasa ta tanada da ake kira FOI a takaice ta shigar da wasikar neman bayanin kan kudaden. Kungiyar ta bayyana cewa kasancewar Najeriya daya daga cikin kasashen da suka sa hannu a taron Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da cin hanci da rashawa haki ya taraya a wuyanta na tabbatar da ganin ana bin wannan doka sau da kafa a cikin kasar.

"Kungiyar ta fada a cikin karar cewa, "A matsayin Nigeria na daya daga cikin kasashen da suka sa hannua babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan Yaki da Cin Hanci da Rashawa, da taron Kungiyar Hadin kan Afrika kan yaki da cin hanci da rashawa, da kuma kundin Afrika kan kare hakkin bil'adama da kuma 'yancin 'yan kasa, Najeriya ta amince za ta tabbatar da kyakkyawan kulawa da dukiyar talakawa da kuma bada izinin samun bayanai ba tare da tsangwama ba. Ya kamata a kiyayye wadannan yarjejeniyoyi sau da kafa."

SERAP Ta Nemi Gwamnati Ta Janye Sunayen ‘Yan PDP Da Suka Saci Kudin Najeriya​

An Ba Buhari Wa'adin Kwana Bakwai Ya Bayyana Kadarorinsa​

Martanin 'Yan Najeriya Kan Raba Kudin Da Abacha Ya Boye

Wani abu da ya dauki hankali a karar shi ne yadda kotu ta umurci Shugaba Buhari ya tilasta wa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su ICPC da EFCC su yi hanzari su binciki yadda aka raba wasu kudade har biliyan 51 daga asusun gwamnati a shekara 2019.

EFCC Ta Sake Kama Biliyoyin Naira a Legas

Wannan batu dai ya ja hankali kungiyoyi masu zaman kansu da dama da suka rika yaba shigar da karar. A hirar ta da Sashen Hausa, shugabar wata Kungiya mai zaman kanta da ta ke sa ido tare da yin aiki da hukumar ICPC, Halima Baba Ahmed ta ce wanan shigar da kara abu ne mai kyau domin bai kamata a bari gwamnati ta yi ta tafiya kara zube ba. Bisa ga cewar ta, wannan yunkuri zai taimaka gaya wajen yaki da cin hanci da rashawa wanda in aka bi a hankali zai sa a samu cigaba a kasa.

Dangane da hurumin shigar da kara, kwararre a fanin Kundin tsarin Mulki Barista Mainasara Ibrahim Umar ya ce kungiyar wace gwamnatin Shugaba Buhari ta ba izinin yin rajista, tana da hurumin shigar da kara akan ayyukan gwamnati amma ba ta yi karar shugaban kasa ba. Bisa ga cewarsa, idan kungiyar ta shigar da Shugaban kasa kara to akwai hurumi da shari'a ta ba Atoni Janar na kasa ya je lotu ya janye wannan shari'ar ba tare da bada wata hujja ba.

SERAP tace ta shigar da karar ne domin yan Najeriya na da yancin sanin yadda ake aiwatar da kudaden kasa domin samun fahimta da kara yarda tsakanin gwamnati da al'umar da ta ke mulka.

A shekarar da ta gabata, SERAP ta shigar da kararraki ishirin kan gwamnati tarayya da gwamnatocin jihohi dangane da batutuwa dabam dabam da suka jibinci take hakin bil’adama da kuma ‘yancin ‘yanjarida. Kungiyar ta kuma dauki matakin dakatar da kafa dokar da aka nemi yi a majalisar dattijai da za ta bada dama ga tubabbun ‘yan kungiyar Boko Haram, wadanda a dokar ake so a yi amfani da kudin al’umma a tura su karo ilimi kasashen waje.

Shugaban Majalisar Dattawa ta 9, Ahmad Ibrahim Lawal

A cikin wasikar da ya rubuta wa shugaban majalisar dattijai Dr. Ahmad Lawan ranar 28 ga watan Fabrairu dangane da dokar kula da tubabbun ‘yan kungiyar Boko Haram, mataimakin shugaban kungiyar SERAP Kolawole Oluwadare yace wannan dokar rashin adalci ne kuma zata nuna ba a kula da wahalun da ‘ya’yan kungiyar suka jefa su ciki ba, da kuma irin ta’assar da kungiyar ta’addancin Boko Haram ta yi.

Saurari rahoton Madina Dauda cikin sauti

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG