An Sallami Saif Ali Khan Daga Asibiti

Saif Ali Khan a Mumbai

‘Yan sanda a Mumbai sun ce sun kama wani mutum mai shekaru 30 wanda ake zargi da hannu a harin a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AP.

Rahotanni daga India na cewa, an sallami jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood Saif Ali Khan daga asibiti bayan kammala jinya a asibitin Lilavati da ke birnin Mumbai.

Wani mahari ne ya kutsa gidan Saif ya caka masa wuka har sau shida a gidansa a ranar 16 ga wtaan Janairu, lamarin da ya sa jarumin ya ji munanan raunuka a cewar rahotanni.

Tun daga lokacin aka kwantar da Saif a asibiti inda aka masa aiki.

Likitoci sun yi nasarar curo wani bantaren wuka da tsawonsa ya kai inci 2.5 a wani barin jikinsa.

Bayan kwanaki shida da ya kwashe a asibitin, Saif ya samu sauki an kuma sallame shi a ranar Talata a cewar gidan talabijin mai zaman kansa na ABP News a India.

‘Yan sanda a Mumbai sun ce sun kama wani mutum mai shekaru 30 wanda ake zargi da hannu a harin a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AP.

Mai dakinsa Kareena Kapoor da ‘yarsu Sara Ali Khan ne suka rufawa Said baya a lokacin da yake komawa gida.

Wannan hari da aka kai wa Saif ya matukar girgiza masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood.