A yau Alhamis shahararran jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood a Indiya, Rishi Kapoor ya mutu a Mumbai bayan ya yi fama da cutar sankaran jini na tsawon shekaru biyu.
Jarumin mai shekaru 67 da haihuwa ya fara fitowa a fim din Mera Naam Joker (My Name is Joker) a trance kenan tun yana dan yaro. Ya sami karbuwa a zukata miliyoyin masoyansa tare da labarin soyayya na wani matashi a fim din Bobby a shekarar 1973.
Sai dai labarin mutuwar sa ya kasance mummunan al’amari na 2 ga mana’antar shirya fina-finan Bollywood da kuma miliyoyin masu kallon fina-finan ta, kasancewar Kapoor ya mutu ne kwana daya bayan da fitaccen jarumi Irrfan Khan ya mutu sakamakon cutar daji.
Kapoor ya shafe kusan shekara daya yana jinya a asibiti a birnin New York kafin ya koma Indiya a watan Satumban da ya gabata.
Facebook Forum