An Sako Sauran Daliban Jami'ar Greenfield Ta Kaduna 14 Da 'Yan Bindiga Suka Sace

  • Murtala Sanyinna

Taswirar Kaduna da hoton bindiga

‘Yan bindiga a jihar Kaduna sun sako sauran daliban Jami’ar Greenfield 14 da suka kwashe tsawon kwana 40 a hannunsu, bayan biyan kudin fansa har naira miliyan 180.

A cikin wata sanarwa da jami’ar ta Greenfield da ke Kaduna ta fitar, magatakardan jami’ar Mohammed Bashir, ya tabbatar da cewa an sako dukan sauran daliban jami’ar 14 da wani ma’aikaci daya da ‘yan bindiga suka sace.

Sanarwar ta ce tuni kuma da daliban suka sadu da iyalansu.

A cikin wani hoton bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta na yanar gizo, an nuna wasu biyu daga cikin daliban da aka sako, suna bayyana cewa sai da iyayensu suka biya kudin fansa har naira miliyan 180, kafin ‘yan bindigar su sako su.

A ranar 18 ga watan Afrilu ne ‘yan bindigar suka kai hari a jami’ar ta Greenfield da ke wajen Kaduna kan titin zuwa Abuja, inda suka yi awon gaba da dalibai 23, kana bayan ‘yan kwanaki suka nemi a biya kudin fansa naira miliyan 800 kafin su sako su.

Daliban Kaduna da sace

‘Yan bindigar sun kashe dalibai 3 a ranar 23 ga watan, kwanaki 5 bayan sace su, inda aka sami gawarwakinsu a kauyen Kwanar Bature da ke kusa da jami’ar.

Haka kuma sun kashe wasu 2 daga cikin daliban a ranar 26 ga watan, wadanda su kuma jami’an tsaro suka gano gawarwakinsu a cikin jeji, wanda ya ba da adadin dalibai 5 kenan da suka kashe a yayin tattaunawa da su.

To sai dai wata mata a jihar ta sami ceto dan ta, bayan da rahotannin suka ce ta biya kudin fansar dan na ta naira miliyan 20.

Gwamnatin jihar Kaduna dai ta yi tsaye kaimun cewa ba za ta yi sulhu da ‘yan ta’adda ba haka kuma ba za ta biya kudin fansa ba “ko da kuwa dan gwamna aka sace.”

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Iyayen daliban da aka sace sun yi ta kai ruwa rana da gwamnatin jihar, wacce ma ta yi barazanar hukunta duk wanda ya biya kudin fansa ga ‘yan ta’adda.

To sai dai iyayen yaran sun yi kunnen kashi da umarnin na gwamnati, inda bayan zanga-zanga da nuna fushinsu ta hanyoyi daban-daban, suka shiga tattaunawa da ‘yan bindigar.

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin tattaunawar, ‘yan bindigar sun nemi da a biyawa kowane dalibi kudin fansa naira miliyan 10, to amma dai ba’a kai ga tantance ko nawa ne kowane mahaifi ya biya ba kafin a sako daliban.

To sai dai duk da haka ita ma gwamnatin jihar ta Kaduna ta fitar da sanarwa, inda ta ke bayyana farin cikin ta akan sako daliban.

Sanarwar wadda kwamishinan lamurran tsaron cikin gida Samuel Aruwan ya fitar, ta bayyana fatar cewa “halin ukuba da suka shiga na tsawon makwanni, zai kasance alkhairi wajen gina makomarsu a rayuwa.”

Harin na jami’ar Greenfield dai shi ne irinsa na 2 a jihar ta Kaduna a cikin kasa da watanni 2, domin kuwa a ranar 11 ga watan Maris ma, ‘yan bindiga sun kai irin wannan hari a kwalejin aikin gona da gandun daji ta Afaka a Kaduna, inda suka yi awon gaba da dalibai 39.

Kalejin Fasahar Aikin Gona Da Gandun Daji ta Tarayya Da Ke Kaduna

An sami sako rukunin na karshe na daliban kwalejin su 27 makwanni 2 da suka gabata, bayan sun kwashe tsawon kwanaki 56 a hannun ‘yan bindigar, wadanda rahotannin suka bayyana cewa sai da aka biya su kudin fansa ta miliyoyin naira kafin a sako su.