An Sako Daliban Kaya A Zamfara

  • Murtala Sanyinna

Daliban Kaya a jihar Zamfara.

An sami ceto daliban makarantar sakandaren jeka-ka-dawo da 'yan bindiga suka sace a garin Kaya ta jihar Zamfara.

Rahotanni daga jihar Zamfara na bayyana cewa an sako daliban nan 73 da 'yan bindiga suka sace da rana karin, a wata karamar makarantar sakandaren jeka-ka-dawo da ke garin Kaya ta cikin karamar hukumar mulkin Maradun a jihar Zamfara.

A wani hoton bidiyo da aka saki ta kafafen sada zumunta na yanar gizo, an nuna gwamnan jihar ta Zamfara Bello Mohammed Matawalle ya na tarbon yaran da aka sako, wadanda aka shiga da su a fadar gwamnatin jihar cikin motocin safa-safa.

Gwamnan daga bisani kuma ya yi musu jawabi, tare da bayyana cewa an sako daliban ne ta hanyar wani kakkarfan kwamitin da aka kafa, da ya kumshi jami'an tsaro na dukkan bangarori.

Daliban Kaya a jihar Zamfara

Ya ce kwamitin ya yi amfani ne da wasu tsofaffin 'yan bindigar da suka tuba, da suka yi aiki tare da jami'an tsaro wajen bibiya da gano inda daliban suke, tare kuma da tabbatar da ganin an ceto su.

To sai dai gwamnan bai ba da cikakken bayani kan yadda aka sami ceto yaran ba, wala'alla ko an biya kudin fansa ko an yi artabu da 'yan bindigar ne ko kuma yaya.

Daliban Kaya a Zamfara

To sai dai a jawabin na shi, gwamnan ya ce an sami ceto dukkan yaran da aka sace na Kaya, ba tare ko daya ya salwanta ko cutuwa ba.

A ranar 1 ga watan nan na Satumba ne dai 'yan bindigar suka kai farmaki a makarantar ta garin Kaya da misalin karfe 11 na rana, inda kuma suka yi awon gaba da daliban kimanin 73 da malaminsu.

An kuma sami ceto daliban ne a daidai lokacin da dakarun sojin Najeriya ke ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin 'yan bindigar da ke jihar ta Zamfara da makwabtanta, a yayin da kuma aka rurrufe al'amura da suka hada da kasuwanni, hanyoyi da kuma kafafen sadarwa a jihar.