An Saki Dalibai Da Ma'aikatan Jami'ar Zamfara Da Aka Yi Garkuwa Dasu Bayan  Watanni 7

  • VOA Hausa

Zamfara

Dalibai da ma’aikatan jami’ar tarayya ta Gusau a jihar Zamfara, wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa dasu, sun shaki iskar ‘yanci bayan shafe watannin 7 a hannunsu.

Kwararre kuma mai sharhi akan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ne ya tabbatar da sakin mutanen a rahoton daya wallafa a shafinsa na X a yau Litinin.

An samu rahoton yin garkuwa da mutanen ne yayin wani harin ‘yan bindigar a yankin birnin Gusau cikin watan Febrairun daya gabata.

Sai dai, Zagazola Makama bai yi karin bayani akan yanayin daya kai ga sakin mutanen ba, ko an biya kudin fansa ko akasin hakan.

Ya kara da cewar jami’an tsaro sun taka muhimmiyar rawa wajen kubutar da mutanen.

“An saki dalibai da ma’aikatan jami’ar tarayya ta gusau.”

“An samu rahoton cewar ‘yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai da ma’aikatan jami’a a garin Gusau tun cikin watan Febrairun shekarar da muke ciki, “a cewar Zagazola.

Zagazola ya kara da cewar, “bayan shafe tsawon lokaci a hannun ‘yan bindiga, muna tabbatar da cewar dukkanin wadanda aka yi garkuwa dasu din sun dawo cikin koshin lafiya.”