Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadin Kan Matasa Da Shugabanni Zai Rage Tabarbarewar Tsaro - Kungiyar Connect The Dots


Kungiyar CONNECT THE DOTS
Kungiyar CONNECT THE DOTS

Wani zauren zantawa kan lamuran yau da kullum mai taken “CONNECT THE DOTS” ya karfafa cewa hadin kan matasa da jagorori zai kawo raguwar tabarbarewar tsaro musamman a arewacin Najeriya.

Rashin tsaro na kan gaba wajen matsalolin da ke kawo kuncin rayuwa baya ga ‘dan karen tsadar kayan masarufi a kasar.

A taron da zauren ya gudanar a Abuja matasa da ke da kwarewa wajen fannoni daban-daban da wasu shugabannin al’umma sun zauna a teburi daya inda su ka yi bani gishiri in ba ka manja kan rashin tsaro.

Masu jawabai sun duba tushen tabarbarewar tsaro a arewa maso yamma da ya samar da barayin daji, illar rashin adalci, shan miyagun kwayoyi, bazuwar makamai, aikin ‘yan sa kai da sauran su.

Abba Danmaraya matashi da ya zo daga Kano wanda ke da kwarin guiwa kan cewa hada kai da matasa ne zai kawo maslaha “in a ka cigaba da hada kai a ka cigaba da karatu a ka cigaba da jajircewa wajen cewa mutanen da su ka cancanta su a ka zaba, abubuwan da su ka ta’azzara za su samu saukin su”

Ita ma matashiyar ‘yar siyasa Zainab Buba Galadima ta karfafa cewa sai kowane bangare ya sauke nauyin da ke kan sa kafin samun saukin rashin tsaro da ke hana hatta noma da ke zama kashin bayan tattalin arzikin arewa.

Shugabar zauren CONNECT THE DOTS Halima Abdulra’uf ta ofishin Muryar Amurka da ke Abuja ta ce shaukin ba da gudunmawa don saita ‘yan uwanta matasa ya sa ta shirya taron “ matasan nan wadanda su ke da basirar kirkire-kirkire ne, me ya sa ba a shigowa a dama da su?”

Baya ga malaman addini irin tsohon ministan sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami, Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal na daga bakin da su ka halarta da karin haske kan yanda su ke daukar matakan yaki da barayin daji.

Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami
Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami
Gwaman jihar Zamfara, Dauda Lawal (hagu)
Gwaman jihar Zamfara, Dauda Lawal (hagu)

Hakanan su ma sun saurari shawarwarin yanda za a samu bakin zare daga basirar matasa.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Hadin Kan Matasa Da Shugabanni Zai Rage Tabarbarewar Tsaro - Kungiyar Connect The Dots
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG