WASHINGTON, D. .C. - Kevin Adam Kinyanjui Kangethe ya tsere ne a lokacin da yake jiran a mika shi kan sammacin Massachusetts bisa zarginsa da kashe budurwarsa tare da barin gawarta a mota a filin jirgin sama na birnin Boston. A makon da ya gabata ne ya zame daga ofishin 'yan sanda ya shiga cikin wata karamar mota.
An kama Kangethe ne a Embulbul, gundumar Kajiado da ke wajen babban birnin kasar Kenya a yammacin ranar Talata yayin da yake neman mafaka a daya daga cikin gidajen 'yan uwansa, in ji Shugaban 'yan sandan Nairobi Adamson Bungei.
"Mun sake kama shi kuma mun gode wa duk wadanda suka taimaka a wannan aiki," in ji shi.
An kuma dakatar da jami’ai hudu daga bakin aiki a ofishin bayar da rahoto a ranar da ya kubuce, suna jiran matakin ladabtarwa kuma suna iya fuskantar tuhuma.
‘Yan sandan jihar Massachusetts sun ce a farkon watan Nuwamba ne dai Kangethe ya bar gawar budurwarsa a mota a filin tashi da saukar jiragen sama na Logan inda bayan nan ya shiga jirgi zuwa Kenya.
Jami’an Massachusetts sun ce sun yi aiki tare da hukumomin Kenya domin gano shi, kuma an kama shi a wani kulob na rawa a ranar 30 ga watan Janairu bayan ya kwashe watanni uku yana gudun hijira.
Wani jami’in ‘yan sanda ya shaidawa AP cewa Kangethe ya ce ya yi watsi da ‘yancin zama ‘dan kasar Amurka.
-AP