Sa’adu Mogoggo, wanda aka kashe wa mahaifi da kuma kanne biyu a wannan hari, ya ce baya ga kashe 'yan uwansa da suka yi, maharan sun yi awon gaba da shanu da kuma kona musu dukiya.
Tun ranar alhamis ne aka fara wannan tashin hankalin sakamakon takaddamar da ta taso game da filayen da aka sayarwa Fulanin da ke yankin, wanda kuma kawo yanzu a ke ci gaba da samun hare-hare.
Hon. Bashir Muhammad da ke wakiltar yankin a majalisar dokokin jiha a tabbatar da faruwar lamarin, inda ya mika kokon bararsu da a kara tura karin jami’an tsaro don kare rayuka da kuma dukiya.
A wata sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun gwamnan jihar, Emmanuel Bello, ya yi Allah wadai da faruwar lamarin a yanzu.
A bangare guda, al’ummomin yankin da ake kai wa hare-hare sun yi barazanar fice wa daga Najeriya muddin gwamnatin kasar ba ta kula da rayukansu ba.
Ko a watan Yunin shekarar da ta gabata, yau kimanin watanni 10 sai da aka samun irin wannan tashin hankali a yankin, lamarin da ya tilastawa dubban mutane gudun hijira zuwa Kamaru baya ga rayukan da suka salwanta.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibarhim Abdul’ziz.
Your browser doesn’t support HTML5