An Saka Dokar Hana Zirga-zirga a Wasu Yankunan Jihar Pilato

Zanga Zangar kin jinin SARS a Jos

Gwamnatin jihar Pilato ta saka dokar hana fita na tsawon sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta kudu, har sai yadda hali ya yi.

A wani jawabi da gwamnan jihar Pilato Simon Lalong ya yi wa al’ummar jihar, biyo bayan rikicin da ya faru a wasu sassan jihar, gwamnan ya ce mutane uku sun rasa ransu yayin da aka kona motoci da lalatawa da satar dukiya da kuma kone wurin ibada guda a yakin Gero, dake garin Bukur a karamar hukumar Jos ta kudu.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa a jihar Pilato, Mista Dan Manjang ya ce dokar ta shafi kowa banda masu gudanar da ayuka na musamman kamar jami’an asibiti da ‘yan kwana-kwana da jami’an tsaro.

Shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa, Shehu Bala Usman ya ce jama’a su dora kan zaman lafiya da aka samu a yankin Jos.

Wata hatsaniya da ta tashi a titin Ahmadu Bello Way daura da Kasuwar Terminus a tsakiyar birnin Jos hedikwatar jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya tayi sanadin rasa dukiyoyi.

Zanga zangar EndSARS a Jos

Bayanai na nuni da cewa rigimar ta tashi ne bayan da wasu masu zanga-zangar #EndSARS suka nemi kafa shinge a wata mahada da ke kasuwar da wasu muhimman sassan kasuwanci da ke kan titin Ahmadu Bello Way, sai wasu matasa da ke kasuwanci a wurin suka nuna rashin amincewarsu.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

An Saka Dokar Hana Zirga-zirga a Wasu Yankunan Jihar Pilato - 3'01"