An Sace Limamin Addinin Krista Dan Asalin Kasar Italiya A Niger

Rahotanni daga yankin Makalondi dake kan iyakar jamhuriyar Niger da kasar Burkina Faso sun ce wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wani mai wa’azin addinin krista dan asalin kasar Italiya a daren jiya Litinin, yayinda hukumomi ke cewa an tura jami’an tsaro domin su ceto shi.

Bayyanai sun yi nuni da cewa a wajejen karfe 9 na daren jiya Litinin ne wasu ‘yan bindiga dake kan babura suka dira gidan mai wa’azin addinin krista din da ake kira Pier Luigi Maccali, mazaunin kauyen Bamoanga dake nisan kilo mita 25 da garin Makolandi kusa da iyaka da Burkina Faso.

Kakakin kungiyar ‘yan kato da gora Habibu Umaru ya bayyana cewa hukumomin jamhuriyar Niger wadanda suka tabbatar da aukuwar lamarin sun bayyana cewa an tura jami’an tsaro domin kubuto Pier Liugi daga hannun ‘yan bindigan da suka nufi kasar Burkina Faso da shi.

Karkarar Makollandi na daga cikin wuraren dake fama da matsalar tsaro a yankin Tilabery a ‘yan shekarun nan. Garin na fuskantar hare hare daga kungiyoyin ta’addanci dake da sansani a kasar Mali.

Your browser doesn’t support HTML5

An Sace Wani Malamin Krista Dan Asalin Kasar Italiya A Nijer 2'13