Maharan sun bude wuta a kan makarantar Bethel Baptist High da ke jihar Kaduna da safiyar Litinin, inda suka yi awon gaba da akasarin dalibai 165 cikin dare.
Malaman makarantar sun shaida wa manema labarai cewa ba su san inda aka kai daliban ba.
‘Yan sanda a jihar Kaduna sun ce sun ceto mutane 26, ciki har da malami daya.
Satar ranar Litinin na daya daga cikin sace-sacen mutane da dama na baya-bayan nan, galibi don neman kudin fansa, wadanda suka addabi makarantu a arewacin Najeriya.
A karshen watan da ya gabata, wasu ‘yan bindiga sun kai hari wata makaranta a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar, inda suka yi awon gaba da akalla dalibai 80 da malamai.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ruwaito kimanin makarantu 600 a arewacin Najeriya sun rufe sakamakon ci gaba da kai hare-hare tun karshen shekarar da ta gabata.
A farkon wannan shekarar, gwamnati ta yi alkawarin samar da karin tsaro a makarantun. Amma malamai da masu fafutuka a kasar sun ce makarantunsu ba su da kariya sosai.
Mahukuntan Najeriya sun fuskanci karin suka kan sace-sacen, daya daga cikin kalubalen tsaro da dama a kasar da suka hada da rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabas, da kuma yunkurin ballewa daga ‘yan aware da ke ci gaba a kudu maso gabashin.
Iyayen Daliban Da Aka Sace A Najeriya, Aun Gudanar Da Addu’o’i
Your browser doesn’t support HTML5