Rahotanni daga jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya na cewa, an rufe jami’ar da ke jihar bayan da hukumomi makarantar suka lura ana samun karin wadanda cutar coronavirus ke harba.
Kafafen yada labaran kasar da dama sun ruwaito cewa, matakin ya biyo bayan wani zama da majalisar jami’ar ta gudanar, wanda ya amince da bukatar a rufe makarantar.
Jaridar Premium Times ta yanar gizo ta ruwaito cewa shugaban kungiyar malaman jami’ar ASUU, Dele Ashiru, ya tabbatar mata da daukan wannan mataki.
Karin bayani akan: ASUU, Babajide Sanwo-Olu, Premium Times, coronavirus, COVID-19, jihar Legas, Nigeria, da Najeriya.
Bayanai sun kuma yi nuni da cewa daga ranar 26 ga watan Yuli, dalibai za su koma yin karatu daga gida ta yanar gizo.
A cewar jaridar Vanguard, shugaban sashen kula da al’amuran dalibai Mr. Ademola Adeleke ya fada cikin wata sanarwa cewa, daukan matakin ya zama dole duba da yadda cutar take yaduwa a sassan makarantar.
Legas, ita ce ta fi kowacce jiha yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus da adadin mutum 60, 638 yayin da take da adadi mafi yawa na wadandan suka mutu wanda ya kai mutum 456.
A farkon makon nan, gwamna Babajide Sanwo-Olu ya gargadin cewa, jihar na fuskantar barazanar yiwuwar samun karin yaduwar cutar a karo na uku.