Tuni Kungiyar mamallaka makarantu masu zaman kansu ta bukaci ma’aikatar ilimi da shugabanin makarantun da abin ya shafa da su bi hanyoyin warware wannan takaddama cikin ruwan sanyi don kada lamarin ya shafi karatun yara.
Makarantu masu zaman kansu akalla 36 ne hukumomi suka rufe bayan da bincike ya gano su da wasu tarin laifukan da ke barazana ga sha’anin karatun boko.
Makarantun za su ci gaba da zama a rufe har zuwa lokacin da suka cika ka’idodin aiki a cewar ministan ilimi Pr Ibrahim Natatou.
Kungiyar mamallaka makarantu masu zaman kansu wace ta nuna damuwa akan wannan mataki, ta bukaci bangarorin su bi hanyar sulhu.
Sai dai kungiyoyin kare hakki a fannin ilmi na ganin matakin gwamnatin ya yi daidai, bisa la’akari da cewa bude makarantu kara zube wani al’amari ne da ka iya tabarbarar da sha’anin ilimi.
Shugaban kungiyar COADDE Amadou Roufai Lawan Salao na cewa za su zuba ido domin tabbatar da cewa ba'a bijirewa doka ba.
Matakin wanda aka fara zartar da shi nan take, ya shafi makarantun faramare da sakandare masu zaman kansu a jihohin Zinder Maradi Dosso da Yamai.
A cewar hukumomin ilimi doka ta yi tanadin hukuncin zaman gidan yari na makwanni 2 zuwa watanni 3 da tarar cedi 50,000 zuwa 500,000 ga duk wanda aka samu da laifin bude makarantar boko ba tare da samun lasisi ko kuma wata takardar izini daga mahukunta ba.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5