Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye Da kashi 80 Cikin Dari Na Malaman Makaranta A Ghana Suka Fadi Jarabawar Lasisin Koyarwa


Wasu Yaran Makaranta
Wasu Yaran Makaranta

Faduwar fiye da kashi tamanin cikin dari na malaman makaranta a Ghana na jarabawar lasisin koyarwa ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar musamman tsakanin masu ruwa da tsaki inda wasu ke ganin wannan babban barazana ce ga tsaron kasar.

KUMASI, GHANA - A shekarar 2018 ne aka gudanar da jarabawar baiwa malaman makaranta lasisi wato Teacher Licensure Exams a Ghana domin tabbatar da inganci tareda kwarewar malamai da suke horas da yaran makaranta a kasar.

To sai dai wannan yunkurin na karfafa sashen neman ilimi a kasar, yana fuskantar koma baya sosai sakamakon ci gaba da faduwa a jarrabawar da malaman keyi.

Alkaluma sun nuna cewa daga cikin malamai 7,728 da suka rubuta jarrabawar a watan Mayun bana, 6,551 sun fadi, wato kashi 83.5 cikin dari ke nan suka kasa cin jarabawar.

Hakan ya sa Dennis Osei Owusu, Sakataren Majalisar Malamai ta kasa NTC a takaice, ya bayyana cewa wannan babbar barazana ce ga tsaron kasar Ghana.

Ya ce " ina kallon wannan a matsayin babbar barazana ga tsaron kasa saboda wadannan sune malaman da za su shiga azuzuwa su horas da yaranmu. Har in aka sami damar duban yadda wasunsu suka gabatar da amsoshin tambayoyin, to za ka tambayi kanka, ta ya ya ma aka yi suka shigo wannan sashen."

Sir. Bashiru Shehu mai sharhi kan lamurran ilimi kuma shugaban makarantar sakandare ta Ibadu Rahman a Kumasi, ya alakanta faduwa jarrabawar da malaman makarantun suka yi da rashin nazari tare da rashin tsari wajen shirya jarrabawar.

Ya ce "ana tura malaman bayan sun kammala koleji wasu makarantu su yi hidimar kasa kafin su dawo su rubuta wannan jarrabawa. Wasu kafin su dawo sun manta da abubuwa da yawa, na biyu wasu malaman basu iya yin nazari."

Ita kuwa cibiyar da ke baiwa gwamnatocin nahiyar Afrika shawara kan harkar neman ilimi tare da al’adu Africa Center For Edcation and culture, ta bukaci gwanati da ta sake duba tsarin koyar da malamai a kasar muddin tana neman kawo karshen wannan matsala.

Saeed Sulaiman shugaban cibiyar ya ce "Idan gwamnati na so ta shawo kan wannan matsala, ya kamata a duba ayi gyara a kolejojin horas da malamai a duk fadin kasar saboda lamarin da ban mamaki a ce kashi tamanin da uku cikin darin wadanda suka rubuta jarabawar da zasu koyar sun fadi. Akwai matsala kuma ya kamata a duba ta fannin kolejojin."

A nata bangare kungiyar hadin gwiwar malamai ta kasa wato GNAT a takaice, ta ce wannan matsala ce da ta shafi kasa kuma ya kamata masu ruwa da tsaki su yi zama a teburin shawarwari su tattauna domin ganin wannan alamarin bai faru ba kuma.

Thomas Musah, sakataren kungiyar ya ce "la'akari da abin da ke faruwa a yanzu, wane bayani za'a yi ma masu biyan haraji a kasar? Muna kira da a yi zama tsakanin masu ruwa tsaki.”

Kawo yanzu dai majalisar malamai ta kasa da take da alhakin shirya jarabawar ta ce ta bullo da tsarin bunkasa ci gaban malaman domin tabbatar da cewa an sami kwararru da za su dinga horas da dalibai a makarantu.

Saurari cikakken rahoto daga Hamza Adam:

Fiye Da kashi 80 Cikin Dari Malaman Makaranta A Ghana Suka Fadi Jarabawar Lasisin Koyarwa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG