An Rantsar Da Shugaban Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Gabon

Shugaban juyin mulkin Gabon Janar Brice Oligui Nguema a lokacin rantsar da shi

A ranar 30 ga watan Agusta, mintuna kadan bayan sanarwar Bongo ya lashe zabe, sojoji karkashin jagorancin Janar Oligui Nguema ya karbe mulki.

WASHINGTON, D.C. - Jami’an soji da wasu jami’ai ne suka yi wa Nguema tarba a lokacin da ya isa wurin bikin, kuma bayan nan kwamitin alkalan kotun tsarin mulkin kasar suka rantsar da shi.

Gidan talbijin na kasar ya nuna hotunan taron jama'a da ke ta murna da kuma wasu dakaru masu sulke suna harbi a cikin ruwan cikin teku.

A cikin wani jawabi da ya yi, Nguema ya gabatar da bukatar samar da sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar da za a amince da shi ta hanyar kuri'ar raba gardama, da sabbin dokokin zabe, da kuma matakan baiwa bankuna da kamfanoni fifiko don bunkasa tattalin arziki.

Ya kuma ce za a yi maraba da ‘yan siyasa da suka yi gudun hijirar tare da ‘yanto fursunonin siyasa.

Ya bayyana juyin mulkin, wanda ya kawo karshen mulkin shekaru 56 da iyalan Bongo suka yi a kasar mai arzikin man fetur, a matsayin wani lokaci na ‘yantar da kasa.

Libreville, Gabon, Aug. 30, 2023.

“Idan shugabanni suka murkushe mutane...sojoji ne ke mayar musu da martabarsu,” inji shi. "Mutanen Gabon, yau lokacin farin ciki da kakanninmu suka yi mafarki ya tabbata."

Wasu jiga-jigan gwamnatin Bongo da suka hada da mataimakin shugaban kasa da Firai Minista ne suka halarci bikin.

Har yanzu Bongo na karkashin daurin talala.

An zabe shi ne a shekara ta 2009, inda ya karbi mulki daga hannun mahaifinsa marigayi Omar Bongo wanda ya hau mulki tun daga shekarar 1967.

Masu adawa da shi sun ce iyalan ba su yi adalci ba wajen raba arzikin man fetur da ma'adinai na Gabon ga al'ummar kasar mai mutane miliyan 2.3.

-Reuters