Taron dai ya gudana duk da watsi da sakamakon zaben da daya daga na kan gaba a ‘yan takarar Alhaji Sa’idu Maikano ya yi da ke cewa an tafka magudi.
Kungiyar Miyetti Allah MACBAN a takaice dai ita ce mafi girman kungiyoyin makiyaya a Najeriya da ke karkashin Sultan din Sokoto da taimakon Sarakunan Katsina, Kano da Lamidon Adamawa.
Sabon shugaban kungiyar Baba Usman Ngelzarma ya yi alwashin sauya fasalin kungiyar ta hanyar kara shigar lamuran zamani da ilmantar da makiyaya da ke dazuka ilimin boko.
Ngelzarma ya tabo batun samun hannun wasu matasan makiyaya cikin satar mutane da hakan ya ke kawo zullumi a yankin arewa maso yamma; inda ya ce zai dau matakan magance kalubalen ta hanyar jawo gaggan masu hannu alamarin da wayar da su kan illar hanyar da su ke kai.
In za a tuna a zantawa ta musamman mai kaluabalantar sabbin shugabannin Sa’idu Maikano ya ce matukar a ka rantsar da su zai garzaya kotu.
A halin yanzu dai Baba Ngelzarma na kira ga samun goyon bayan kowa amma duk da haka ya musanta saba ka’ida a zaben.
Hakika samun shugabanci mai karbuwa a Miyetti Allah na da muhimmanci wajen inganta lamuran kiwon shanu a Najeriya da yaki da sashen fitinar satar mutane da fadan manoma da makiyaya.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5