Hindatu ‘yar shekaru 25, da hauhuwa ta dare mukamin ne bisa umurnin gwamnatin jihar a zaman shugabar karamar hukumar mai rikon kwarya biyo bayan rusa majalisun kananan hukumomin jihar da gwamnatin jihar ta yi a sakamakon karewar wa’adin mulkin su.
Sai dai wannan mataki na gwamnatin jihar ya janyo cece-kuce da musayar ra’ayoyi mabanbanta tsakanin jama’ar karamar hukumar, yayin da yawanci ke alakanta lamarin da al’ada kokuma addinin yankin, kmar yadda jama’a da dama suka bayyana cewa a ganin su, akwai lauje cikin nadi.
Duk da haka dai akwai jama’a da dama da suka yi na’am da wannan sabon ci gaba, wadanda suka yi tururuwa suka rufa mata baya sa’adda ta kai ziyara fadar mai girma sarkin Kebbin Argungu jim kadan bayan an rantsar da ita.
Shi kansa sarkin Kebbin argungu Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera, ya yi kokarin ankarar da jama’ar karamar hukumar da su rungumi sabuwar al’adar wadda ba sabun ba, wadda a cewar sa bata sabawa ka’ida ba.
Wannan lamari da yazowa jama’ar yankin wani abin bazata, domin sabon abu ne mata su rike irin wannan mukami a yankin Kebbi, da Sokoto da jihar Zamfara.
Ga Rahoton Murtala Faruk Sanyinna Daga Sokoto.
Your browser doesn’t support HTML5