An Rabawa Asibitoci Kudade a Gombe

FILE

Kwamitin asusun tallafa wa wadanda ta’addancin ‘yan bindiga ya shafa a Najeriya ya kai ziyara Jihar Gombe a Najeriya, inda ya kai gudun muwar kudade Nera miliyan 40 da aka rabawa asibitoci guda biyu. Wadannan asibitoci sun hada da na gwamnatin Tarayya, da kuma na Jiha.

Tun da farko kuwa, shugaban kwamitin Farfesa Victor Osheshe ya shaida wa gwmanan Jihar Ibrahim Hassan Dankwambo makasudin ziyarar kwamitin.

Mr. Victor yace kwamitin ya je ne domin ya sadu da gwamnatin Jiha, da kuma wasu cibiyoyin dake tunkarar illolin da matsalolin rashin tsaro ke haddasawa.

Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Dankwambo ya bayyana farin ciki, da kuma godiya dangane da azama ta gaggawar bada tallafi ga mutanen da suka tagayyara.

Dan Kwambo yace abunda asusun yayi na karfafa gwiwa ne, sannan yace za’a alfahari da wannan asusu a Najeriya baki daya. Ya kara da cewa zai yi amfani da wannan damar domin godewa gwmanatin Tarayya dangane da bada agaji iri daban-daban.

Daya daga cikin shuwagabannin asibitocin da suka amfana daga wannan asusu Abubakar Sa’idu ya ji dadin gudun muwar “an bamu miliyan 20. Zamu siyo kayan aiki”.

Your browser doesn’t support HTML5

An Rabawa Asibitici Kudade a Gombe – 3’55”