Gamayyar kungiyoyin mata Musulmin da suka hada da FOMWAN da kuma kungiyar masu kare mata Musulmi sun gudanar da taron ne da nufin fadakar da al’umma da kuma cimma daidaito kan matakan da ya kamata a dauka wajen kare lafiyar al’umma da bata sabawa addini ba.
Kungiyar tace amfani da hijabi da ‘yan harin kunar bakin wake ke yi, wadansu lokuta su badda kama suyi shigar mata da hijabi yana janyowa mata Musulmi tsana da sa shakku a zukatan jama’a.
Manufar taron itace ankarar da kasa kan kiraye kirayen da wadansu kungiyoyi ke yiwa hukumomi na ganin an hana matan amfani da suturar da suka amfani da ita bisa ga koyarwar addinin Islama.
Ra’ayoyin mahakarta taron dai sun banbanta a kan wannan batu, yayinda wadansu suke ganin daukar wannan matakin ya sabawa addinin Islama, wadansu kuwa suna gani ba lallai ne ayi amfani da hijab ba wajen rufe jiki.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu Abdulwahab Mohammed ya aiko mana daga Bauchi.