Jihar Naija tayi wani kokarin azo agani, Hajiya Hajo Sani wata Jami’ar kungiyar da ke kula da lafiyar iyali, tayi muna garin haske dangane da mahimmanci amfani da gidan sauro don kare lafiyar al’umah. Ta kara da cewar, an lura da cewar wannan gidan sauron na da matukar mahimanci don haka yasa aka kara yawan wannan gidan sauron da aka rabas, a wannan karon da ya kai kimanin miliyan biyu da dubu dari bakwai 2.7
Ta bakin uwargidan gwamnan jihar, Hajiya Jummai Babangida Aliyu, wadda ita ta kaddamar da wannan rabon gidan sauron. Ta kuma ce amfani da wanna gidan sauron zai taimaka wajen rage yawan mace macen yara harma da na manya. Shi kuma Dafta Usman Muhammad darakta a matakin farko a ma’aikatan lafiya ta jihar Naija.
Yace zazzabin cizon sauro na haddasa bari ga mata masu juna biyu, ya kuma yi bayani akan yadda mutane zasuyi amfani da gidan sauron ta yadda yakamata, su tabbatar cewar sun rufe koina ta yadda sauro ba zai samu damar shigaba.
Your browser doesn’t support HTML5