Bayanai na nuni da cewa bular anobar zazzabin Ebola tayi kamari a kasar Saliyo, duk da cewa ta sassauto a wasu kasashen Afrika ta yamma.
Kungiyar Lafiya ta duniya tace kasar Saliyo ta tabbatar cewa a karshen watan jiya na Nuwamba, mutane 537 aka tabbata sun kamu da cutar a kasar, karin fiye da mutane 150 ke nan cikin mako guda.
Bayani na baya bayan da aka gabatar Laraban nan, kungiyar Lafiya ta Duniya tace anobar tafi kamari a birnin Freetown inda aka bada rahoton fiye da mutane maitan sun harbu da kwayar cutar.
Kungiyar tayi bayani cewa fiye da mutane dubu 17 ne suka kamu da cutar a duk fadin duniya, Kuma ya zuwa yanzu cutar ta kashe kimamin mutane dubu 6 da 70.
Rahoton na kungiyar lafiya ta duniya yace an samu sasautowar bular anobar a kasar Guinea wadda ta bada rahoton cewa mutane 77 suka kamu da cutar a makon jiya. Kasar Liberia kuma ta bada rahoton cewa mutane 43 ne suka kamu da cutar.