Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaduwar Cutar Ebola ta Ragu


Gwada Cutar Ebola a Najeriya.
Gwada Cutar Ebola a Najeriya.

Bayan ta kashe fiye da mutane dubu shida a kasashen yammacin Afirka, yanzu yadwar cutar ta ebola ta ragu

A jiya Litinin Hukumar Lafiya Ta Duniya ta bada wani labari mai dadin ji wanda ba kasafai take bada irin shi ba game da mummunar cutar Ebola mai kisa, wadda ta hallaka mutane fiye da 6,000 a yankin Yammacin Afirka. Kyakkyawan labarin shi ne cewa yaduwar cutar na raguwa.

Hukumar ta ce burin da ta sa a gaba na killace kashi 70% na masu cutar da kuma yi mu su magani a kasashen Laberiya da Saliyo da kuma Guinea kafin daya ga watan nan na Disamba ya na kan turba.

Mataimakin shugabar Hukumar, Bruce Aylward ya ce ya shaidawa manema labarai a Geneva cewa sakamakon hakan ya sa an fara cike gibin dake tsakanin cutar da kuma shawo kan ta. Amma ya kara da cewa da sauran aiki tukuru kafin a kai ga cewa wadannan kasashe uku sun rabu da cutar Ebola.

Aylward ya ce duk da wannan ci gaba da aka samu, har yanzu jama'a na bukatar ci gaba da dabi'un wanke hannu da sabulu akai-akai da kuma tsoma kafafun su cikin bokitan ruwan sinadarin Chlorine mai kashe kwayoyin cuta.

A jiya Litinin Hukumar Lafiya Ta Duniya ta sake bibiyar kundin bayanan ta na yawan mace-macen da aka yi a yankin, ta ce akwai wasu mace-mace dubu daya da aka alakanta da cutar Ebola bisa kuskure.

A karshen watan Nuwamba Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce kasar Guinea kawai ce ke kan turbar dakile saurin yaduwar cutar kamar yadda aka sa a gaba.

A cewar Hukumar Lafiya Ta Duniya, cutar Ebola na kashe kashi 50% na wadanda ta kama, wato rabin wadanda suka kamu da ita mutuwa suke yi.

XS
SM
MD
LG