Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yace an samu cigaba a yakin da ake yi da ebola amma yayi gargadin cewa har yanzu akwai jan aiki a gaba.
Yace da alamu masu kamuwa da cutar sun ragu a wasu wuraresanadiyar matakan kwarai da ma’aikatan kiwon lafiya suka tsara kuma suna bi sau da kafa.
To saidai kuma a wasu sassan ana samun karuwar masu dauke da cutar.
Akwai wasu wuraren da cutar ke kara yaduwa. Yace sabili da haka ana bukatar taimakon kasashen waje da kwararrun likitoci da masu aikin kiwon lafiya na sa kai.
A kauyuka aka fi bukatar taimako domin nan ne cutar take barna yanzu sabili da rashin isassun ma’aikatan kiwon lafiya.
Yadda cutar ke yaduwa yanzu abun damuwa ne musamman a kauyuka, inji Ban Ki-moon.
Daraktan Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya Margaret Chan tace kusan mutane 500 ne ake sawa ido a kasar Mali inda tuni bakwai suka rigamu gidan gaskiya