A ranar litinin 19 ga watan Oktoba ne hukumar kare hakkin bil’adama ta Najeriya wato NHRC ta mika rahoton bincike da ta yi akan korafe-korafen take hakkin bil’adama da jami’an ‘yan sanda na SARS suka yi ga ministan shari’ar kasar.
Ministan Sharia’ar Najeriya, Abubakar Malami ya ce ya karbi kofi na rahoton hukumar kare hakkin bil’adama ta Najeriya da ta dauki matakin na bin bahasi, kuma ta shirya rahoto na abin da ta gani ko ta fahimta kan irin zargin da ake yi na cin zarafin al’umma da ‘yan sandan SARS suka yi.
Amma ba a kai gaba na daukar mataki ba kan ‘yan sandan da ake zargi da keta hakkin bil’adama.
Malami ya kara da cewa ofishinsa zai bi bahasi da kadi idan akwai bukatar karin bincike za’a dauki matakin kara bincike idan akwai bukatar daga bangaren gwamnati na dogaro da rahoton gaba daya za ta sanar da abin da ya kamata.
Ya ce gwamanti ta saka hannu kan wasu dokoki da suka hada da Police Act wadanda suke da nasaba da ‘yan sandan al’uma wato community police da kuma inganta aikin ‘yan sanda.
Har ila yau dai gwamanti ta saka hannu akan dokar samar wa ‘yan sanda kayan aiki na gari wato Police Trust Found.
A makon da ya wuce, hukumar kare hakkin bil’adama ta Najeriya, ta kafa kwamitin binciken tsoffin jami’an SARS mai zaman kansa, domin gano gaskiya a kan koke-koken ‘yan kasar na take hakkin bil’adama.
Hukumar ta NHRC ta mika rahoton binciken da ta gudanar ta hannun baban sakatarenta, Tony Ojukwu, tare da wasu muhimman abubuwa, tana mai ra’ayin cewa Atoni janar Malami zai duba yadda za’a hukunta masu laifi a shari’ance.
A wani bangare kuwa, Ministan Yada Labarai da Al’adu na Najeriya, Lai Muhammad, ya bayyana cewa babu zanga-zangar da ta samu gagarumin nasara kamar ta #EndSARS#, ya na mai nuna yakinin cewa za a samu sauyin da ake fafutuka a kasar.
Sannan ya kuma kara da cewa za’a kawo gabar da mutunta hakkin bil’adama zai zama ginshiki ga komai tare da neman masu zanga-zanga su ba wa zaman lafiya dama.
Sai dai har yanzu ana cigaba da gudanar da zanga zanga a wasu biranan sassan kasar da ake kira #EndSARS# da a wasu wurare ta rikide ta zama tashin hankali, inda tuni wasu gwamnonin jihohi suka kafa dokar hana fita.
Saurari cikakken rahoton Halima AbdurRa’uf:
Your browser doesn’t support HTML5