Sojojin kasa da kasa da ke kasar Mali sun kama Shebani Ould Hamma wanda hukumomin jamahuriyar Nijer ke zargi da aikata hare-haren ta'addanci
WASHINGTON, DC —
Sojojin hadin guiwar kasashen duniya sun cafke Shebani Ould Hamma wani kasurgumin dan ta'addan da jamahuriyar Nijer ke nema ruwa a jallo. Sojojin na kasa da kasa sun kama shi ne tsakanin Kidal da Gao, a arewacin kasar Mali.
Shebani Oild Hamma shi ne wanda hukumomin kasar jamahuriyar Nijer ke zargi da aikata hare-haren ta'addanci a kasar Nijer, har ma da harin da aka kai gidan kason birnin Niamey a ranar daya ga watan yunin da ya gabata wanda ya zama sanadin mutuwar sojojin kasar ta Nijer guda biyu. Baicin asarar rayukan sojojin biyu da aka yi wasu dimbin 'yan kaso sun yi amfani da damar da suka samu lokacin harin suka sulale. Hukumomin kasar jamahuriyar Nijer na zargin cewa an kitsa makircin kai harin ne domin a kubutar da Shebani Ould Hamma wanda ke tsare a gidan kason na Niamey a lokacin. Wakilin Sashen Huasa a birnin Niamey, Abdoulaye Mamane Amadou ya aiko da karin bayani akan nasarar da sojojin suka yi suka kama dan ta'adda Shebani Ould Hamma.

Your browser doesn’t support HTML5