Tsohon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Abdurrahman Bello Dambazau, shi ne ya bayyana wannan a lokacin da yake hira da Muryar Amurka.
Janar Dambazau yace rashin shugabanci na kwarai a kasashenmu na Afirka, na haddasa cin hanci da rashawa, da kawo koma bayan tattalin arziki, da lalata harkar ilmi da kyautata jin dadin al'umma, abubuwan da su kan taru su kara wutar tashin hankali.
Game da batun rashin tsaro, musamman a yankin arewacin Najeriya, Janar Dambazau yace tilas sai an samu hadin kan kasashe makwabtan Najeriya domin kuwa ta cikin wadannan kasashe makwabta ake shigo da makaman da 'yan ta'adda da 'yan fashi ke amfani da su.
Janar din yayi misali da cewa tsawon bakin iyakar Najeriya da kasashe kamar Kamaru da Chadi da Nijar ya kai dubban kilomitoci, amma kuma tasoshin bakin iyaka guda 57 tak Najeriya take da su. Alhali kuma akwai barayin hanyoyi fiye da dubu daya da dari biyar wadanda ake amfani da su wajen shiga da fita daga kasar.