WASHINGTON, DC —
Matan Shugabannin kasashen Afirka sun shirya wani taron wuni guda a Nyamai babban birnin Janhuriyar Nijar kan yaki da tallar magunguna bisa titi da al’amarin ya yi yawa a akasarin kasashen Afirka.
Wakilinmu a Janhuriyar Nijar Abdullahi Mamman Ahmadu ya ce yawancin masu sana’ar sayar da magungunnan ba su ma san komai game da magani ba. Ba su da wata sana’a shi ya sa suka rungumi sana’ar sayar da magungunan duk kuwa da hadarin da ke ciki, ganin har ma akan sayar da magungunan da likitoci yakamata su bayar da shawarar ko a sha ko a’a. Yace an shaida masa cewa saboda saukinsu da kuma matsin rayuwar da jama’a ke ciki ya sa ake ta sayen irin wadannan magungunan duk kuwa da hadarin da ke tattare da hakan.
Wata babbar jami’a a Ma’aikatar Lafiya Ta Janhurtiyar Nijar mai suna Dr Maryama Sambo ta ce harkar magani na da ka’idoji sosai ta yadda sam sam bai dace ba wadanda ba su yi karatunsa ba su shiga sayar da shi saboda abu ne da ya shafi lafiyar dan adam.
Shi kuwa Malam Ikade Ibale, Sakataren Zartaswar Matar Shugaban Kasar Nijar Malika Isuhu Mahammadu, wadda hasalima kungiyar ta ce ta kira wannan taron, ya ce an saka matan shugabannin kasashen Afirka ne cikin harkar saboda su na da matukar tasiri kan jama’a musamman ma mata da matasa.