An Kirkiro Manhajar Da Za Ta Taimakawa Matuka Keke

Direbobin mota na iya amfani da manhajoji daban-daban da za su nuna masu hatsari ko cinkoso a kan titi ta yadda za su iya kauce masu.

Amma ga matuka keke da ke tafiya akan hanyoyi kamar motoci, sai abinda hali ya yi. A saboda haka, wani dalibi a wata jami’a da ke Ingila ya kirkiro wata manhaja da za ta taimakawa masu tuka keke da kananan hukumomi nuna masu munanan wurare, a cewar rahoton wakiliyar Amurka Faith Lapidus wakiliyar VOA.

Sunan manhajar "Flare", kuma ta na kama da wata na’urar lantarki da za a makala a hannun keke.

Amma Jake Thompson, wani dalibi mai kere-kere a jami’ar Sussex, ya ce akwai abubuwa guda 3 a jikin na’urar da za su ba mai tuka keke damar sanar da duk wata matsala da ya ci karo da ita a kan hanya.

Duk abin da mai tuka keke ya latsa a manhajar zai isar da sakon wurin da matsalar take zuwa wata manhajar waya.

Bayan matuki ya isa inda zai , sai ya tabbatar da irin kalubalen da ya fuskanta ta manhajar ya kuma bada karin bayani. Ana iya yin amfani da wannan bayanin wajen sa shi a cikin taswirar hanyar.