Shugabar kungiyar tallafawa marayu da gajiyayyu dake jihar Kano Malama Nafisa Ahmad Awal ta ce, bana kungiyar Ashnaf da ke tallawafa marayu da gajiyyayu ta samu tsaiko wajan tallafawa marayu musamman ma a wannan wata mai alfarma na ramadana sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasa.
Ta ce bisa al’ada a farkon azumi suke fara bada tallafi ga marayu sai ga shi a bana an kai rana ta biyar shiru babu amo ba labari sakamakon rashin samun tallafi daga wasu bayin Allah da suka saba bada tallafinsu a kowacce shekara
Malama Nafisa ta ce a yanzu ba basu sami wannan tallafi ba amma zasu duba asusu su na kudin da suke tarawa a kai akai su kuma duba yiwuwar tallafawa wadanda suka dace, sakamakon wannan aikin lada da suka saba yi.
Ta kara da cewa akalla suna da kimanin mutane tamanin da suke tallafawa da kayan abinci da na sallah mussamam ma ga yara marayu domin suma su zama tamkar sauran yara.
A daya bangaren kuwa mun waiwayi wannan batu na mata da suke maida hankali wajen bada himma ga ayyukan gida suke kuma mantawa da ibadunsu a wannan lokaci, inda muka zanta da malama Maryam Abubakar Abba, wacce ta ce ba laifi bane idan mace ta maida hankali ga girke-girke don farantawa mijinta rai amma yana da alfanu ta tsara komai.
Malama Maryam Abubakar Abba, ta ce idan mace ta tsara ayyukan gida lallai zata sami falalar ibada a wannan lokaci na ramadana gami da samun ladar hidimtawa maigida.
Saurari cikakkiyar hirar a nan.
Facebook Forum