Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karon Farko Fadar Sarauniyar Ingila Za Ta Yi Amarya Bakar Fata


Yayin da auren yarima Harry da Meghan Markle ke gabatowa, an samu labarin cewa yarima Charles mahaifin yarima harry, shi zai hanunta Amarya Meghan a fadar Kensington a Ingila.

Mahaifin Meghan Thomas, ba zai samu damar halartar auren diyar sa ba saboda rashin lafiyar da ya kai har aka masa aiki a zuchiyar sa.

Ms Markle ta fitar da sanarwa jiya Alhamis cewa tana fatan cewa mutane za su baiwa mahaifinta sararin maida hankali kan samun lafiya

Yarima Wales ya yi marhaba da auren dan sa da Meghan, inda ya saka musu albarka a cewar fadar.

Kakan Yarima Harry da ake kira Duke of Edinburgh zai halarci bikin auren da za a yi gobe Asabar.

Mahaifiyar Meghan, Doria Ragland, zata kai ‘yar ta cocin da za a daura auren da ake kira St George’s chapel a yankin Windsor.

Kuma Mahaifiyar amariyar zata hadu da Sauraniyar Ingila, karo na farko a fadar Windsor inda Ango yarima Harry dan shekaru 33 da amaryar sa Meghan yar shekaru 36 za suyi mata rakiya zuwa ganin sarauniyar.

Za a fara bikin da karfe 12:00 na rana agogon Ingila kuma za’a a yadda a kafofin yada labarai a fadin duniya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG