A yayin da ake jajibirin watan ramadana, kamar kowacce shekara DandalinVOA zai mai da hankali ne wajen kawo muku shiri na mussaman da ya danganci azumin watan ramadana, kama daga hidimomin mata, yanayi na kasuwanci, abinci lafiyar da al’umma, duk a lokacin azumi da sauransu.
Kasancewar yau ita ce rana ta farko mun samu zantawa da wata ma’aikaciya Malama Hauwa Hadeja, wacce ta ce wannan lokaci ne da mata ma’aikata ya kamata su jajirce wajen kammala ayyukan gida akan lokaci cikin tsari da nastuwa.
Ta ce a yanzu dole mata su zamo masu lissafi wajen kammala ayyukan gida da wuri, domin a wasu lokutan ma kafin su tafi aiki ya kamata su rage wasu ayyukan gida, don idan sun dawo kada aiki ya cakude musu.
Malama Hauwa, ta ce duk da cewar ana baiwa mata dama wajen daga sassauta masu a wuraren ayyukansu, mafi akasari a jihohin Arewacin Nijeriya, hakan wata dama ce ta rage musu hidimomin azumi a gidajen su.
Shi ma a nasa bangaren mun ji ta bakin Limamin Masallacin Triumph, dake Kanon Nijeriya, wanda ya ce bisa tsari ana gobe za'a fara azumi, ba’a so ayi azumi a wannan rana an so a sha ruwa a kuma jira watan ramadana.
Ya ce yana da kyau mutum ya kwana da niyyar azumin ramadana, kuma ana so musulmi ya yi sahur domin sunnah ce mai karfi, ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar.
Facebook Forum