Kwamishinan tsaron cikin gida Samuel Aruwan ya fada a wata sanarwa da ya fitar cewa, rahotanni sun nuna cewa, ‘yan fashin dajin sun gamu da ajalinsu ne yayin wani artabu da suka yi da sojojin kasar.
“An kashe ‘yan bindigar ne a wani fitaccen tsaunin da ake kira Maikwandaraso da ke karamar hukumar Igabi.” In ji Aruwan.
Sanarwar ta kuma ce an samu nasara akan ‘yan bindigar ne ta hanyar hadin gwiwar dakarun sama da na kasa.
“‘Yan fashin dajin hudu da aka kashe sun hada da Alili Bandiro, Dayyabu Bala, Bala Nagwarjo da Sulele Bala.”
A cewar Aruwan, yayin arangamar, an kuma kashe wasu da yawa daga cikin mabiyansu.
Yayin da aka gabatar masa da rahoton wannan nasara, Gwamna Malam Nasiru El Rufai ya nuna farin cikinsa tare da jinjinawa dakarun Najeriya kan matakan da suke dauka na fatattakar ‘yan fashin dajin daga maboyarsu.
Tsaunin Maikwandaraso na kusa da kauyen Karshi yana kuma da iyaka da dazukan Kawara da Malul wadanda dazuka ne da suka yi kaurin suna wajen zama maboyar ‘yan bindiga wadanda duk suke karamar hukumar ta Igabi.