An Kashe Sojojin Nijar Shida A Wani Hari Kan Bututun Mai Tsakanin Nijar Da Benin

Yan bindiga

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, wanda shi ne na farko kan jami’an tsaron dake kare bututun mai.

Wasu mahara da ba a san ko su waye ba a Jamhuriyar Nijar sun kai hari kan sojojin da ke gadin babban bututun mai tsakanin Nijar da Benin a ranar Laraba, inda suka kashe sojoji shida, kamar yadda wasu majiyoyin tsaro uku suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Alhamis.

Sai dai wata majiya ta ce bututun bai lalace ba.

NIGER-OIL

Harin da aka kai kan ‘yan sintiri da ke aikin kare bututun mai ya faru ne a tsakanin kauyukan Salkam da Tibiri, a yankin Dosso da ke kudu maso gabashin Nijar a ranar Laraba da yamma.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, wanda shi ne na farko kan jami’an tsaron da ke kare bututun mai.

Dukkan majiyoyin uku sun ce an kashe sojoji shida.

A watan Nuwamba ne aka kaddamar da bututun mai na kusan kilomita 2,000 da kasar China ke marawa baya, wanda zai hada rijiyoyin mai na Agadem na Nijar da gabar tekun Benin inda ake lodin danyen mai domin fitar da shi zuwa kasashen waje.