WASHINGTON, D.C. - An kai harin ne a ranar Talata a yankin kudu maso yammacin kasar da ke kan iyaka da Burkina Faso mai tazarar kilomita 60 daga Yamai babban birnin kasar, in ji ma'aikatar tsaron kasar, inda ta kara da cewa sun kuma kashe maharan 100 da ta kira 'yan ta'adda.
Ma'aikatar ta ce, "matakin gaggawar da sojoji suka dauka da kuma martanin da jiragen sama da suka yi amfani da shi a wurin da aka gwabza fadan ya ba su damar shawo kan lamarin.”
Nijar kamar sauran kasashen yankin Sahel na yammacin Afirka, ta kwashe shekaru tana fafutukar ganin ta shawo kan masu tada kayar baya masu alaka da Al-Qaida da IS da suka kashe dubban mutane, suka kuma tilastawa miliyoyi kauracewa gidajensu da kuma haddasa karancin abinci.
Ganin cewa gwamnatocin farar hula ba za su iya shawo kan wannan matsala ba na daya daga cikin abubuwan da suka haifar da juyin mulki a yankin, ko da yake a Nijar manyan jiga-jigan sojojin da suka kwace mulkin kasar matakin siyasar cikin gida ce.
Jami’an tsaron fadar shugaban kasa karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani, su ne suka hambarar da shugaba Mohamed Bazoum, kuma har yanzu suna ci gaba da tsare shi, inda suka bijirewa matsin lamba daga Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka da kuma kasashen yammacin Turai na mayar da shi kan karagar mulki.
-Reuters