Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe ‘Yan Ta’adda 55 A Wani Aikin Hadin Gwiwa A Nijar


Sojojin Nijer hade da na Faransa.
Sojojin Nijer hade da na Faransa.

Rundunar sojan Nijar ta ce an kashe mayakan jihadi 55 da suka hada da wasu manyan mayaka masu alaka da kungiyar I.S a wani samame na hadin gwiwa da Najeriya.

Sanarwar ta ce, a farmakin na kwanaki 22, wanda ya kawo karshe a ranar Lahadin da ta gabata, an auna wata maboyar 'yan ta'adda ta Daesh a yammacin Afirka (ISWAP) a garin Arege da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya da ke kan iyaka da Nijar.

'Yan ta'adda 55 da aka kashe sun hada da manyan kwamandidi da dama da kuma shugabannin addinai da dama, in ji ta, suna amfani da kalmar gargajiya ga masu jihadi.

An bayar da wannan alkaluman ne a cikin sanarwar da sojoji suka fitar kan ayyukan da suka yi a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijar, wanda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya gani a ranar Litinin.

Sanarwar ta kara da cewa, aikin da ya hada da sojojin sama da na kasa an shirya shi ne da nufin "ci gaba da matsin lamba" kan ISWAP da kuma yanke hanyoyin samar da kayayyakinta.

Sojoji biyu ne suka mutu sannan uku kuma suka samu raunuka, an kuma lalata motoci 13 da babura 13 da kuma “motoci masu sulke” guda biyar.

XS
SM
MD
LG