Kafofin yada labaran kasar Spain, sun ce an kashe mutumin da ake zargi da kitsa harin da aka kai kasar, mai suna Moussa Oukabir, bayan wata musayar wuta da suka yi da ‘yan sandan kasar.
Rahotannin sun ce Oukabir, na daya daga cikin mutane biyar da aka kashe wadanda duk ake zargi da kai harin garin Cambrils dake bakin gabar teku, sa’oi bayan da wata mota ta kutsa cikin mutane a birnin Barcelona a ranar Alhamis, inda mutane 13 suka rasa rayukansu.
Wani jami’in tsaro a kasar ta Spain, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa Oukabir, wanda shi ake zargi da tuka motar, na daya daga cikin mutane biyar da aka harbe har lahira a garin na Cambrils.