Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Daular Larabawa Hudu Sun Mutu a Hatsarin Jirgin Sama


Kafofin yada labaran gwamnati a Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce sojojin daular su 4 sun mutu a lokacin da wani jirgin sama mkai saukar ungulu ya fadi a kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran WAM ya fada yau asabar cewa sojojin suna daga cikin wata rundunar da Sa’udiyya take jagoranci, dake yakar ‘yan tawaye ‘yan mazhabin Shi’a a Yemen.

Kamfanin dillancin labaran na WAM yace jirgin ya fadi a lardin Shabwa na kudancin kasar inda jiragen yakin Amurka suke kai farmaki a kan ‘yan kungiyar al-Qa’ida na kasar.

Rundunar da Sa’udiyya take jagoranci tana yakar ‘yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran ta sama da kuma ta kasa.

‘Yan tawayen sun kwace birnin Sana’a a shekarar 2015, suka tilastawa gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita ta yi hijira zuwa kasar Sa’udiyya, kafin ta komo birnin Aden mai tashar jiragen ruwa a kasar ta Yemen.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG