TARABA, NIGERIA - Iliyasu Mai Riga na daya daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya, bayan da aka kai musu hari, wanda ya ce wadanda ake zargi cewa ‘yan kabilar Tiv ne suka kai har suka kashe mutane biyu nan take, amma shi ya sami tsira daga bisani yaje asibiti don jinya.
Shi kuwa Zuza Audu Kuta wanda alamarin yayi sanadiyar kashe masa kani ya ce lamarin ba dadi kam, amma haka Allah ya nufa, saboda haka ya kamata gwamnati ta shigo cikin lamarin domi a kawo karshen wanna rikicin kabilanci da ya dade ana fama da shi a fadin jihar Taraba baki daya.
Rumande Inburu shugaban karamar hukumar ta Wukari ya ce yanzu haka kura ta lafa a rikicin kuma gwamnati na yin duk abin da ya kamata don ganin an kawo karshen wanna tashin hankali na kabilanci da ya addabi yankin na Wukari.
Kakakin rudunar 'yan sandan jihar Taraba SP Usman Abdullahi Jada ya ce rudunar ta yi kokarin dakatar da bazuwar rikichin, yanzu haka kuma kwamishinan ‘yan sadan jihar ta Taraba ya ba da umurnin gaggawa da ayi bincike domin gano sanadiyar wannan rikici.
Saurari Cikakken Rahoto Daga Lado Salisu Garba:
Your browser doesn’t support HTML5