Rundunar ‘yan sandan Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin.
Mai magana da yawun 'yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, cikin sanarwar da ta aikewa Muryar Amurka ta ce tun ranar Asabar ne rikicin ya faro a 3rd Avenue da ke cikin unguwar ta Gwarimpa, al'amarin da ya sa aka yi gaggawar aikewa da ‘yan sanda don samar da zaman lafiya.
Wasu mutane biyu sun sami mummunan rauni, wanda bayan kai su asibiti dayan ya cika a daidai lokacin da likitoci ke kokarin ceto ransa sakamakon raunuka da ya samu.
Mai rikon mukamin kwamishinan ‘yan sandan birnin Abuja, DCP Ahmed Musa, tuni ya yi ganawar gaggawa da shugabannin Gwarawa da Hausawa a ofishinsa don lalubo hanyar samar da zaman lafiya.
'Yan sandan wadanda a halin yanzu suka kaddamar da bincike don gano musabbabin faruwar rikicin sun ce sun kama wasu da ake zargi, kana an jibge karin jami'an tsaro da ke sintirin tabbatar da tsaro a yankin.