Arangama tsakanin yan Sanda Masar da masu zanga zangar wadanda suke jifa da duwatsa ta shiga rana ta biyu harma mutane takwas sun mutu fiye da dari uku kuma sunji rauni.
Sojojin Masar suna ta jifan masu zanga zangar daga kan wani gini dake kusa da Majalisar wakilan kasar a birnin Alkahira kuma sunyi amfani da bututun feshi domin tarwatsa mutane. Masu zanga zangar wadanda ke bukatar a kawo karshen mulkin soja a kasar sun sa shingaye domin su kare kansu.
A jawabin daya gabatar da gidan talibiji na kasar, Prime Minista Kamal El Ganzouri yace jami’an tsaro suna kokarin ne su kare gine gine. Yawancin yan kasar suna son a kawo karshen tarzomar haka nan,
Wannan tarzoma ta barke ne a yayinda yan kasar suke jiran sakamakon zagaye na biyu na zaben wakilan Majalisar wakilai da aka yi a wannan mako. Alamu sun nuna cewa jam’iyun Islama suna kara yawan wakilai bisa nasarar da suka samu a baya. Yau Lahadin nan idan Allah ya yarda ake sa ran baiyana sakamakon zaben