Jami'an gwamnati a Sudan ta Kudu sun ce an kashe mutane kusan hamsin a wani harin ramuwar gayya wanda ya samo asali daga zaman gaba da fada da ake yi a tsakanin wasu kabilu biyu.
Hukumomi suka ce an fara fada na baya-bayan nan litinin da daddare a lokacin da 'yan kabilar Murle dauke da makamai suka kai farmaki a kan wani kauye na 'yan kabilar Lou Nuer dake gundumar Duk a bangaren arewacin Jihar Jonglei mai fama da fitina.
Wannan shi ne karo na biyu da 'yan kabilar Murle suke kai hari a kan kabilar Lou Nuer cikin kasa da mako guda.
Jami'an gwamnati suka ce wannan harin ramuwar gayya ce ta wani babban farmakin da 'yan kabilar Lou Nuer suka kai kan yankunan kabilar Murle a karshen watan da ya shige. 'Yan kabilar Lou Nuer su kimanin dubu 6, sun kai hari a kan garin Pibor da wasu yankuna na kabilar Murle a watan Disamba. Jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka ce an kashe mutane da yawa.
Sudan ta Kudu ita ce kasa ta baya-bayan nan da ta zamo 'yantacciya a duniya, amma tana fama da mummunan tashin hankali na kabilanci da kuma fada a tsakanin gwamnati da kungiyoyin 'yan tawaye tun daga ranar samun 'yancinta.
Har ila yau, kasar tana kokarin samo hanyar kula da 'yan gudun hijira daga kasar Sudan da kuma rikicin da take yi da Sudan kan bakin iyaka da kuma kudaden shiga na man fetur. Wannan tankiya ta haddasa fargabar barkewar yaki a yankin.